BBC News Hausa (@bbchausa) 's Twitter Profile
BBC News Hausa

@bbchausa

BBC Hausa - Fiye da shekara 60 na labaran duniya da rahotannin da suka shafi rayuwarku

ID: 18168536

linkhttp://www.bbchausa.com calendar_today16-12-2008 18:29:17

112,112K Tweet

2,5M Followers

46 Following

BBC News Hausa (@bbchausa) 's Twitter Profile Photo

Cikin rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya kan matsalar shan taba sigari a shekarar 2025, hukumar ta ce akwai ƙasashe 110 a duniya waɗanda suka ƙi mayar da hankali wajen faɗakar da al’umma kan illar sigari duk da ɗimbin asarar rayuka da take haddasawa a kowace shekara.

Hakan na zuwa ne bayan bayanan sirri da aka kwarmata sun nuna cewa hare-haren da Amurka ta kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran ba su yi gagarumar illa ga cibiyoyin ba. Ƙarin bayani - bbc.in/3HQWsin

Hakan na zuwa ne bayan bayanan sirri da aka kwarmata sun nuna cewa hare-haren da Amurka ta kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran ba su yi gagarumar illa ga cibiyoyin ba.

Ƙarin bayani - bbc.in/3HQWsin
BBC News Hausa (@bbchausa) 's Twitter Profile Photo

A cikin wata ukun shekarar da ta gabata ne ƴansanda suka fitar da rahoton kashe mutum 263 da ƙungiyoyin ƴan daba suka yi a yankin Cape na Afirka ta Kudu. Sashen binciken kwakwaf na BBC Africa Eye ya gudanar da bincike kan hakan a unguwanni mafiya hatsari a birnin.

BBC News Hausa (@bbchausa) 's Twitter Profile Photo

Ƴansanda sun yi arangama da masu zanga-zangar waɗanda suka taru a birnin Nairobi suna rera waƙoƙin ''Dole Ruto ya sauka''. Masu zanga-zangar sun yi yunƙurin kutsawa gidan Shugaban ƙasar, William Ruto, kodayake ƴansanda sun dakatar da su. Ƙarin bayani - bbc.in/4kVHYfv

Ƴansanda sun yi arangama da masu zanga-zangar waɗanda suka taru a birnin Nairobi suna rera waƙoƙin ''Dole Ruto ya sauka''.

Masu zanga-zangar sun yi yunƙurin kutsawa gidan Shugaban ƙasar, William Ruto, kodayake ƴansanda sun dakatar da su.

Ƙarin bayani - bbc.in/4kVHYfv
BBC News Hausa (@bbchausa) 's Twitter Profile Photo

Shugaba Trump ya haƙiƙance cewa hare-haren da Amurka ta kai sun tarwatsa tashoshin nukiliyar na Iran, kodayake wasu bayanai sun nuna akasin haka Karin bayani - bbc.in/440EQcp

Shugaba Trump ya haƙiƙance cewa hare-haren da Amurka ta kai sun tarwatsa tashoshin nukiliyar na Iran, kodayake wasu bayanai sun nuna akasin haka

Karin bayani - bbc.in/440EQcp